Me hukuncin kotu kan damar sauya sheƙa ke nufi ga ƴansiyasa?

    • Marubuci, Muslim Muhammad Yusuf
    • Aiko rahoto daga, BBC Hausa
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 4

A ranar Laraba ne wata Babbar Kotun Tarrayar Najeriya ta soke wa'adin da hukumar zaɓen ƙasar INEC ta gindaya wa jam'iyyun siyasa na gabatar da kundin rajistar mambobinsu, inda ta mayar da wa'adin zuwa watan Satumban 2026.

A baya, INEC ta umarci jam'iyyun siyasa su gabatar da kundin sunayen mambobinsu da bayanansu kafin ranar 10 ga watan Mayu domin su samu damar shiga zaben 2027.

Amma yanzu kotu ta ce jam'iyyun suna da damar ci gaba tattara bayanan har zuwa watan Satumban 2026.

A yayin yanke hukuncin da jam'iyyar matasa ta Youth Party ta shigar, mai shari'a M. G. Umar, ya rushe wasu sharudda da INEC ta gindaya gabanin zaɓen na 2027.

Masu fashin baƙin siyasa na yi wa hukuncin kotun kallon wata dama da ta rage wa fusatattun ƴansiyasa ficewa daga jam'iyyun da suke tunanin ba su yi musu adalci ba, musamman a lokutan zaɓukan fitar da ƴantakara da jam'iyyu ke gabatarwa.

Abin da hukuncin kotun ya ƙunsa

Waɗanda suka shigar da ƙarar sun buƙaci kotu ta yanke hukunci kan ko INEC na da hurumin kakaba wa'adin da jam'iyyu za su iya gudanar zaɓukan fitar da gwaninsu, ko gabatar da sunan ɗantakara ko sauya shi da kuma wallafa sunayen ƴantakara da wa'adin yaƙin neman zaɓe.

Mr Umar ya amince da buƙatar jam'iyyar matasan, inda ya yanke hukuncin cewa INEC ba ta da ikon gindaya yadda jam'iyya za ta gudanar da tsare-tsarenta na cikin gida.

Ya yanke hukuncin cewa sashe na 29, 82 da 84 (1) na dokar zaɓe ta 2026 ta ce INEC na da damar sanin lokacin da jam'iyyu za su gudanar da zabuƙan fitar da ƴantakaransu kuma ta sanya ido tare da ƙarbar sunayen ƴantakara, amma ba a ce ta tilasta musu lokacin da za su kammala zabuƙan ba.

A saboda haka alƙalin ya ce INEC ba ta da hurumin yin abin da ya saɓa da dokar zaɓen.

Ya ce dokar zaɓe ta ba da dama ga jam'iyyun siyasa cewa suna da wa'adin kwanaki 90 kafin zaɓe wajen gabatar da ƴantakarar su ko sauya su kuma INEC ba za ta ƙi amsar matakin ba.

Kuma ba a amince INEC ta wallafa sunayen ƴantakara sama da kwanaki 60 kafin zaɓe ba.

Har yanzu INEC ba ta ce komai kan hukuncin ba.

Wannan hukuncin na zuwa ne a daidai lokacin da jam'iyyun siyasa a Najeriya ke ta rige-rigen kammala zaɓukan fitar da gwaninsu kafin cikar wa'adin da hukumar zaɓen ta bayar ya cika domin samun damar shiga zaɓen 2027.

A baya dai an gindaya sharaɗin cewa, babu wani ɗantakara da zai iya sauya jam'iyya zuwa wata domin yin takara da zarar an kammala zaɓukan fitar da ƴantakara.

Me hakan ke nufi?

Ƙwararren lauya a Najeriya Barista Abba Hikima ya ce wannan hukunci da kotun ta yanke ya yi daidai da dokar zaɓe domin hukumar INEC ta ɗauki wasu matakai na gaban kanta ne.

Ya ce hakan kuma zai ba ƴan siyasa damar shiga wasu jam'iyyun da suke so muddin bai yi ƙasa da kwanaki 120 da dokar zaɓe ta gindaya ba.

Barista Hikima ya ce rufe rajistar jam'iyar da INEC ta so aiwatarwa a baya yanzu ya buɗe ƙofa ga waɗanda suke da niyyar yin takara a wasu jam'iyyu.

"Wannan [dokar zaɓe] bai ba [INEC] ƙarfi ta canza wani haƙƙi da doka ta ba ƴankasa da jam'iyyun siyasa ba," in ji Baristan

Ya ƙara da cewa wannan hukuncin na zama kamar fassara ce ga dokokin zaɓe da kotun ta yi, kuma abin da ya kamata hukumar zaɓen ta yi aiki da shi kenan.

"Lallai wannan hukunci da kotun ta yi ya fi dacewa da doka, da kuma sanannun ƙa'idojin tafiyar da shari'a".

Ƙofar sauya sheƙa ta buɗe

Tun bayan wannan hukuncin dai jam'iyyun adawa da ƴansiyasa ke ta maraba da matakin, inda aka fara hasashen cewa ƙofar sauya sheƙa za ta buɗe ga waɗanda aka yi abin da bai musu daɗi ba.

Jam'iyyar adawa ta ADC ta yi maraba da hukuncin, inda kakakinta Mallam Bolaji Abdullahi ya ce wannan wata dama ce da za ta buɗe ƙofarsu ga fusatattun ƴansiyasa.

Ita ma jam'iyyar PDP tsagin Tanimu Turaki ta bakin Farida Umar ta ce wannan hukuncin abin a yaba ne, kuma zai ba jam'iyyun adawa damar yin shirin da ba su yi ba tare da karɓar sabbin mambobi.

Jim kaɗan bayan bayyanar wannan hukunci, ɗan majalisar dokokin jihar Kano mai wakiltar mazabar Gwale, Hon. Abdulmajid Isa Umar Mai Rigar Fata, ya sanar da ficewarsa daga APC.

Kamar yadda hadimin Kwankwaso, Saifullah Hassan ya wallafa a shafinsa na Facebook ya ce Mai Rigar Fata ya sauya sheƙa daga APC zuwa jam'iyyar NDC ne inda Rabiu Kwankwaso ya karbe shi a gidansa da ke Abuja.

Sauya sheƙarsa na zuwa ne bayan ya gaza samun tikitin APC domin komawa majalisar dokokin Kano a zaɓen mai zuwa.

Mai Rigar Fata na wakiltar ƙaramar hukumar Gwale, inda gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya fito, kuma ya kasance ɗaya daga cikin fitattun 'yan siyasar yankin.

An fara zaɓen Mai Rigar Fata a shekarar 2023 ƙarƙashin jam'iyyar NNPP, kafin daga bisani ya bi gwamna Yusuf zuwa APC.